Ghana ta rage kudin aikin hajjin shekarar 2025 zuwa Cedi 62000

0
66

Sakamakon karatowar lokacin rufe karbar kudin aikin hajji a kasashe daban daban mahukuntan kasar Ghana sun sanar da rage kudin aikin hajjin da maniyyatan kasar zasu biya daga Cedi 75, 000 zuwa Cedi 62000, kuma kudin ya tasamma adadin kudin Nigeria naira 6,608,000.

:::Kotu ta sake hana Sarkin Kano na 15 gyara gidan Nassarawa

Daman shugaban kasar mai ci a yanzu John Mahama, ya dauki alkawarin rage yawan kudin aikin hajjin da al’ummar Musulmai ke biya don saukaka musu.

Ragin kudin yazo a daidai lokacin da al’ummar Nigeria ke yin kukan tsadar kudin aikin hajjin wanda ya zarce naira miliyan 8, kamar yadda hukumar aikin hajji ta kasa ta sanar kwanakin baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here