Har yanzu nine shugaban kungiyar APC X Eagle—Ahmad Gogel

0
35

Rikicin cikin gidan daya dabaibaye kungiyar APC X Eagle, ya dauki wani sabon salo a daidai lokacin da dakataccen shugaban kungiyar Ahmad Gogel, ya bayyana cewa har yanzu shine jagoran kungiyar, tare da yin watsi da takardar da aka fitar mai nuni da cewa yanzu ba shine shugaba ba.

Ahmad Gogel, ya bayyana hakan a yau lokacin da yake zantawa da Daily News 24, akan fitar wata sanarwa mai dauke da sanya hannun Najib Bala Shu’aibu, Kabir Waya, Muhktar Kabir, da Farouk Dan Batta, wanda sune suka sanar da dakatarwar.

Sanarwar dakatarwar tace Ahmad Godel da sakataren sa M.I Tudun Wada, sun yi amfani da matsayin su wajen aikata abubuwan da basu cancanta ba, tare da yin alkawarin nada shugabannin rikon kwarya nan gaba kadan.

Sai dai a yayin da yake mayar da martani akan dakatarwar Gogel, yace ba’a bi ka’ida ba wajen dakatarwar saboda ba kwamitin ladabtawar APC X Eagle, ne ya sanar da daukar matakin ba.

A yayin tattaunawar Daily News 24, tayi da Gogel, ya mika sakon sa na bayar da hakuri ga Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, bisa wasu kalaman da suka furta akan sa, inda yace Sarki ba zan siyasa bane, uba ne ga kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here