Yan sanda sun kama mutane 165 da suka shigo Nigeria ba bisa ka’ida ba

0
65

Rundunar yan sandan kasa reshen jahar Kebbi, ta sanar da kama wasu bakin haure su 165, wanda suka shigo Nigeria ba bisa ka’ida ba.

Mutanen da aka kama sun shigo Nigeria ne daga ƙasashen ƙetare 5 rainon kasar Faransa, wanda tuni aka mika su hannun hukumar shige da fice ta kasa NIS, domin fadada bincike.

Mai magana da yawun rundunar SP Nafiu, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar.

Sanarwar tace yan sandan sun samu bayanan sirri dake cewa wasu mutane sun shigo jihar Kebbi, wanda suke da yawan daya zarce 200 kuma baki dayan su suna zaune ne a wani gida mai dakuna uku, a unguwar Kuwait dake birnin Kebbi.

SP Nafiu, yace mazauna unguwar Kuwait, ne suka kai rahoton mutanen har aka samu nasarar kama 165, daga cikin su.

Binciken yan sandan ya ce mutanen sun kasance yan kasashen Niger, Mali, Burkina Faso, Benin, da kuma Ivory coast, wanda suka shigo Nigeria babu wani cikakken dalili.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here