Kungiyar APC X Eagle ta dakatar da shugabannin ta

0
55

Kungiyar yan Twitter, na jam’iyyar APC, wato X Eagle, ta dakatar da shugaban ta Ahmad Gogel, da sakataren sa M.I Tudun Wada.

Bayanin hakan ya fito cikin wata sanarwa mai kwanan watan 4 ga Fabrairu wadda ta samu sanya hannun wasu mutane 4, wato Najib Bala Shu’aibu, Kabir Waya, Muhktar Kabir, da Farouk Dan Batta.

Mutanen sun ce dakatar da shugabannin ya biyo bayan yadda suka aikata wasu laifuka da Kuma yin amfani da mukamin su wajen yin abubuwan da basu cancanta ba.

Mutanen da suka fitar da sanarwar sunce an dauki matakin dakatarwar don cigaban jam’iyyar APC baki daya.

Haka zalika sanarwar tace nan gaba kadan za’a sanar da zabar shugabannin rikon kwarya na Kungiyar APC X Eagle, don cigaba da gudanar da ayyukan ta kamar yadda ta saba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here