Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta kama wani dattijo mai kimanin shekaru 75, mai suna Baba Nuhu, da zargin siyar da kayan maye ga matasa tsawon shekaru 2.
Daily News 24, ta rawaito cewa mai magana da yawun hukumar Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, hakan a yau Talata.
:::A yau ne yan majalisa zasu dawo daga hutu da suka tafi
Maigatari, yace wanda ake zargi ya amsa laifin da ake tuhumar sa da aikatawa na cinikin kayan maye ga matasan unguwar da yake rayuwa, a kauyen Tumbau dake karamar hukumar Gezawa, yana mai cewa wannan itace sana’ar daya dogara da ita wajen yin rayuwa.
Bayanin hukumar ta NDELA, yace wannan abu daya faru akan Baba Nuhu, ya tabbatar da cewa ta’ammali da miyagun kwayoyi ya shafi mutane da dama cikin su har da masu manyan shekaru.
Daga cikin kwayoyin da aka samu a wajen tsohon akwai Tramadol, Diazepa, Exol da sauran su.