Kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta jingine batun yin zanga-zangar data shirya gudanawar a fadin Nigeria, don nuna kin amincewar ta akan yadda gwamnatin tarayya ta sahalewa kamfanonin sadarwa su kara kudin kiran waya dana data da kaso 50, cikin dari.
:::Tallafin Naira biliyan 150 ne yasa gwamnan Kaduna ke goyon bayan Tinubu—El-Rufa’i
Janye gudanar da zanga-zangar da kungiyar ta shiya aiwatarwa a yau Talata, ya biyo bayan tattaunawar da suka yi da sakataren gwamnatin tarayya a jiya Litinin, a birnin Abuja, da yace gwamnati zata duba bukatar kungiyar kwadagon.
Kamfanonin sadarwar kasar nan sunce tashin farashin kayan masarufi ne ya sanya su neman karin kudin da suke cajar abokan hulda dasu.
Da farko NLC, ta nemi a janye karin da mayar dashi wanda bai wuce na kaso 5 ba, ko tayi zanga zanga a kaf fadin Nigeria don nuna kin jinin hakan.
Shugaban kungiyar kwadagon ta kasa Joe Ajaero, ya bayyanawa manema labarai cewa sun janye gudanar da zanga-zangar ce sakamakon gwamnatin tarayya tayi alkwarin kafa wani kwamiti mai karfi da zai bibiyi baki dayan maganar karin kudin kiran wayar.