Tallafin Naira biliyan 150 ne yasa gwamnan Kaduna ke goyon bayan Tinubu—El-Rufa’i

0
38

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, ya kaddamar da Caccakar magajin sa Uba Sani, akan yadda yake bayyana goyon bayan sa ga shugaban Nigeria Bola Tinubu, yana mai cewa bukatar kai da kai ce tasa gwamnan ke nuna goyon bayansa ga shugaban kasar.

Caccakar da tsohon Gwamnan na Kaduna ke yiwa Uba Sani, tazo a matsayin mayar da martani ga kalaman Gwamnan Kaduna mai ci a yanzu lokacin wata tattaunawa da akayi dashi a kafar talbijin ta TVC, inda ya bayyana cewa yana yin mamakin yadda wasu daga cikin wadanda aka kafa jam’iyyar APC, dasu ke kalubalantar Tinubu.

:::Masu arziki ne suke amfanar tallafin wutar lantarkin da muke biya duk wata—Gwamnatin Tinubu

Uba Sani, yayi zantawar ce a ranar litinin data gabata.

Sai dai a yau Talata, El-Rufa’i, ya wallafa wani sako a shafin sa na X inda yace duk wannan goyon bayan da Uba Sani, ke bayyanawa Tinubu, baya wuce dalilin naira biliyan 150, da gwamnatin tarayya ta bawa gwamnatin Kaduna a watanni 18, da suka wuce.

El-Rufa’i, ya kara da cewa a kowacce rana yana ganin abubuwan takaicin da gwamnan ke aiwatarwa, amma duk da haka gwamnatin tarayya ta zabi gwamnatin jihar Kaduna ita kadai domin bata wasu kason kudaden, da babu wata jihar da aka taba bawa tsawon watanni 18, da suka shude.

Tsohon gwamnan Kaduna El-Rufa’i, yace nan gaba kadan idan lokaci yayi al’ummar Kaduna, zasu yi alkalanci da kansu.

Daga cikin kalaman Uba Sani, a lokacin tattaunawar da yayi da TVC, yace abin takaici ne yadda wasu mambobin APC, ke nuna kin amincewa da wasu manufofin Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here