Hukumar kula da ayyukan yan sandan ta kasa (PSC) ta umarci duk wani babban jami’an yan sandan da shekarun sa na haihuwa suka kai 60, ko shekaru 35, yana yin aiki yayi ritaya.
Kakakin hukumar PSC Ikechukwu Ani, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja ranar juma’a inda yace basa bukatar duk wata dokar data sabawa dokar hukumar mai lamba 020908 (i & ii).
Wannan sanarwa tazo bayan shi kansa babban Speton yan sandan kasa Kayode Egbetokun, ya cika shekaru 60, da haihuwa tun a watan Satumba na shekarar 2024.
Shugaban kasa Bola Tinubu, ne ya tsawaita zaman Egbetokun, akan mukamin babban Speton yan sandan kasa, bayan cikar wa’adin kammala aikin sa.
Hukumar kula da ayyukan yan sandan ta kasa ta sanar da hakan a jiya juma’a bayan wani rahoton jaridar Daily trust, dangane da cigaban zaman Egbetokun, akan mukamin babban Speton yan sandan kasa.
Tuni dai wasu ke kalubalantar matakin tsawaita zaman Egbetokun akan mukamin, bisa zargin cewa ko ana kitsa yadda za’a iya yin amfani da shi wajen biyan wata bukatar siyasa a nan gaba.