Shugaban sashin kafafen sada zumunta na Masallacin Sahaba dake unguwar Kundila, bangaren Sheikh Muhammad Bin Usman, Shamsuddeen Sulaiman Usman, yace ko kadan basu amince da dakatarwar limancin da kwamitin Masallacin suka yiwa malamin ba, tare da bayyana hakan a matsayin rashin adalci.
Idan za’a iya tunawa dai a ranar juma’a ne aka samu fitar labarin cewa hukumar gudanarwar Masallacin jami’ur Rahman, wato tsohon Masallacin Sahaba, sun dakatar da Sheikh Muhammad Bin Usman, daga limanci bisa zargin sa da gudanar da hudubar da ka’iya haifar da rikici tsakanin al’umma.
A ranar 24 ga watan Junairu ne Sheikh Bin Usman, ya gudanar da wata hudubar juma’a mai taken “Illar Zalinci” da hudubar ta mayar da hankali akan irin Zalincin da yace anyi masa tun daga farkon kafa Masallacin Sahaba har zuwa yanzu.
A wancan lokaci malamin ya zayyano duk abubuwan rashin dadin da yake zaton kwamitin gudanarwar Masallacin Sahaba suka yi masa na rashin bashi shugabancin Masallacin, tare da bawa wani mutum na daban izinin zama jagora a jami’ur Rahman, tsohon Masallacin Sahaba.
Mai taimakawa Sheikh Bin Usman, a fannin kafafen sada zumuntar, ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Daily News 24, inda yace Marigayi Sarkin Kano na baya Alhaji Ado Bayero, ne ya naÉ—a Malamin a matsayin babban limamin Masallacin Sahaba tun a shekarar 1999.
Yace dalilin komawar Bin Usman yin limanci a Masallacin jami’ur Rahman, shine anzo an nemi ya amince a fadada Masallacin bisa alkawarin shine zai cigaba da zama babban limami, sai dai Shamsuddeen, yace an karya wannan alkawarin tun farkon ranar da aka bude Masallacin saboda ba Bin Usman, aka bawa damar jan Sallar bude Masallacin ba kamar yadda aka saba babban limami ya jagoranci Sallah a ranar da aka bude Masallaci.
Shamsuddeen, yace wannan abu shine dalilin Malam na fitowa cikin huduba ya bayyana gaskiya, wanda hakan ya haifar da kace-nace a cikin masallaci bayan idar da Sallar juma’a a a ranar 24 ga watan Junairu.
Shamsuddeen Sulaiman, ya kara da cewa basu amince da dakatarwar limancin da aka yiwa malamin ba, saboda a cewar sa an zalinci Bin Usman.T
Tuni dai majalisar Malamai ta jihar Kano, ta shawarci Sheikh Muhammad Bin Usman, da ya koma tsohon Masallacin Sahaba, ya cigaba da limanci, wanda, Shamsuddeen Sulaiman, yace sai nan gaba zasu sanar da matsayar su akan shawarar.