Kalaman Ameachi na cewa yan siyasa suna yin kisa rura wutar rikici ne—Matawalle

0
45

Karamin ministan tsaro Bello Matawalle, yace jami’an tsaro sun saka idanu akan Rotimi Ameachi, dangane da kalaman sa na cewa yan siyasa suna yin kisa don su samu damar cigaba da zama akan Mulki.

Rotimi Ameachi, ya kasance tsohon gwamnan jihar Rivers, kuma tsohon ministan Sufuri a gwamnatin Buhari.

Idan za’a iya tunawa a ranar larabar data gabata ne Ameachi, ya bayyana cewa manufar dan siyasar Nigeria itace yayi sata tare da yin kisa don ya samu damar cigaba da zama akan kujerar Mulki, ko da mutane basa bukatar sa.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen taron cigaban shugabanci da tsare tsare, daya gudana a birnin tarayya Abuja.

A yayin taron Ameachi, yace matasa su dena tunanin Tinubu, zai basu mulki salin alin, yana mai cewa sai an tashi tsaye kafin karbar mulki a hannun sa.Sai dai Matawalle, ya mayarwa da Ameachi, martani cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar a jiya Alhamis, inda ya bayyana kalaman Amaechi a matsayin na kawo rikici.

Matawalle, yace bai kamata mutum kamar Ameachi, ya rika yin irin wannan kalamai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here