Dattawan arewa sun yi ala wadai da tsare Farfesa Usman Yusuf a gidan gyaran hali

0
50

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi Allah wadai da kamawa tare da tsare tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa, Farfesa Usman Yusuf, sannan ta bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na ‘yan siyasa domin rufe bakin ‘yan adawa, da masu kalubalantar gwamnati.

Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ne suka kama Yusuf a gidansa na Abuja a ranar 29 ga Janairu, 2025.  

Daga nan ne aka gurfanar da shi a gaban babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya a ranar 30 ga Janairu, 2025. 

Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu na babbar kotun Abuja taƙi amincewa da bukatar belinsa, inda ta ɗage karar da aka shigar domin baiwa EFCC damar gyara tuhumar da ake masa.  

Da yake mayar da martani kan alamarin, mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya bayyana kamun a matsayin wani yunkuri na murkushe muryoyin addawa masu sukar wasu kudire-kudire na gwamnati. 

Kungiyar ta bukaci a gaggauta sakin Farfesa Usman Yusuf, inda ta jaddada cewa a daina danne muryoyin ‘yan adawa domin hakan baya kan tsarin dimokuradiyya.

Farfesan yayi kaurin suna wajen kalubalantar manufofin gwamnatiin Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here