DSS sun gayyaci Sheikh Bin Usman, bayan dakatar dashi daga limanci

0
102

Hukumar gudanarwar Masallacin juma’a na Jami’ur Rahman, wanda a baya aka fi sani da Sahaba, sun dakatar da limamin Masallacin Sheikh Muhammad Bin Usman, biyo bayan gabatar da wata hudubar da aka ce ka’iya haifar da rudani a ranar 24 ga watan Junairu. Malamin ya kasance mai limanci a tsohon Masallacin Sahaba kusan shekara 24, data gabata, da aka gina masa sabo mai suna Jami’ur Rahman, ta hannun AY Maikifi.Gurin da aka gina sabon Masallacin na Jami’ur Rahman, ya kasance inda mutane ke taruwa domin bin Sallar juma’a da Idi, daga Masallacin Sahaba.

Ana tsaka da yin haka AY Maikifi ya gina sabon Masallacin Jami’ur Rahman, bisa cewa za’a bawa Sheikh Bin Usman, damar zama babban limamin sa, tare da dena limanci a Masallacin Sahaba.Sai dai a yayin gudanar da hudubar Sallah a ranar 24 ga watan Junairu, Sheikh Muhammad Bin Usman, ya bayyana yadda aka mayar dashi saniyar ware a fannin limancin Masallacin.

Yace hukumar gudanarwar Masallacin Jami’ur Rahman, ta naɗa limamai uku, ba tare da ayyana shi a matsayin shugaba ba.Rahotonni sun ce hudubar ta sanya wasu daga cikin masu yin Sallah yunkurin farmakar sakataren kwamitin amintattu na Masallacin Abdulkadir Isawa.

Daga haka ne hukumar gudanarwar Masallacin Jami’ur Rahman, ta aikewa da Sheikh Bin Usman, wasikar dakatar da shi daga limanci, inda wasikar tace an dakatar dashi saboda irin kalubalen da hudubar sa ta janyo.

A ranar litinin data gabata ne jami’an tsaron SSS, tare da mahukuntan Masallacin Jami’ur Rahman, suka gayyaci Sheikh Bin Usman, wanda wata majiya tace anja kunnen sa akan ya daina yin hudubar da zata kawo tashin hankali.Haka zalika majalisar Malamai ta nemi Muhammad Bin Usman, ya koma tsohon Masallacin Sahaba don cigaba da limanci, wanda zuwa yanzu ba’a samu labarin ko ya amince da shawarar hakan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here