Tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Ameachi, yace shugaban Nigeria Bola Tinubu, ba zai taba bayar da mulki ga matasa a cikin ruwan sanyi ba, yana mai cewa akwai bukatar yan siyasa su dauki tsauraran matakai don samun nasarar zabe a nan gaba.
Ameachi, ya bayyana hakan ne a lokacin daya halarci wani taron inganta cigaban Dimokradiyya a Nigeria, wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja, da cibiyar cigaban shugabanci da tsare-tsare ta Afrika ta shirya.
Ya kara da cewa babban burin dan siyasar Nigeria ya cigaba da zama akan kujerar mulki ko da kuwa al’umma basa son sa. Yace kamata yayi yan Nigeria su kasance kamar mutanen Ghana da suka canja gwamnati ta hanyar zabe da kuma yin amfani da karfin su, ko za’a kashe su.
Rotimi Ameachi, ya kuma ce dan siyasar Nigeria, bashi da burin daya wuce yin sata da jikkata mutane har ma da yin kisa duk dan ya samu damar cigaba da zama akan kujerar mulki.