Hussaina ta sanar dani Seaman Abbas yana dukan ta—Ahmad Isa, Brekete Family

0
89

Mashiryin shirin Brekete Family, Ahmad Isah, ya tabbatar da cewa Seaman Abbas, yana dukan matar sa Hussaina, wadda tayi iya bakin kokarin ta don ceto shi daga hannun hukumomin rundunar sojin ruwa ta kasa, da suka tsare shi saboda karya ka’idar aiki.

Idan za’a iya tunawa dai batun Seaman Abbas, ya dauki hankalin al’umma a Nigeria musamman arewa, bisa zargin cewa mahukuntan rundunar sojin ruwa ta Nigeria, sun yi masa rashin adalci tare da kulle shi tsawon shekaru saboda yaje yin Sallah ana tsaka da yin wani taro, wanda daga baya aka gano ba haka bane.

Zancen Abbas, ya fito fili kowa ya sani saboda kokarin da matar sa Hussaina, tayi na zuwa shirin Brekete Family, tare da bayyana cewa an yiwa mijin nata rashin adalci.

Daga haka ne batun ya yawata a kafafen sada zumunta har akayi nasarar sakin Seaman Abbas, yayin da sojojin suka sanar da cewa tabbas an kulle shi amma ya aikata danyen laifin daya cancanci a hukunta shi.

Bayan sakin Abbas, ne rundunar sojin ruwa ta Nigeria ta sanar da korar sa daga aiki.

A yanzu kuma wani sabon abin mamaki ne ya kunno kai, na cewa Seaman Abbas, yana duka matar tasa da ta tsaya kai da fata har yakai ga samun yanci ta dalilin zuwa Brekete Family.

Kamar yadda Ahmad Isah, ya shaida cikin shirin sa a jiya Laraba, yace tun a kwanakin baya Hussaina ta sanar da shi cewa Mijin ta yana dukan ta, tare da yan uwan sa, kan zargin an bata tallafin Naira miliyan 20 da mota, ta rike bata bashi ba.

A wancan lokaci a Ahmad Isah, ya nemi Hussaina ta sanar da iyayen ta abinda ke faruwa tsakanin ta da Abbas.Ahmad Isah, yace a lokacin da Hussaina, ta kira shi ta sanar da shi bata da lafiya.

A cikin wannan mako ne kuma Hussaina, ta fitar da wani faifan bidiyon da take cewa tana cikin tashin hankali akan kudin da ake cewa an bata saboda abinda ya faru da Mijin nata, sannan a yanzu ta bar yayan ta da mijin ta a Gombe, inda ta koma Kaduna da zama saboda barazanar da take ciki.

Daily News 24, ta rawaito cewa an wallafa bidiyon da Hussaina, tayi, na cewa ba’a bata kudi ba ya sosa zuciyar mashiryin shirin Brekete Family, inda yace ana zargin sa da cinye tallafin da aka bawa Hussaina.

Ahmad Isah, yace babu mutum daya daya bashi kudi don a bawa Hussaina, tare da cewa zai dena yin shirin Brekete Family, na Hausa saboda zargin da yace anyi masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here