Anyi rikici tsakanin matasa masu kwasar fetur daga motar data fadi da jami’an kwana-kwana

0
46

Wasu matasa sun farmaki jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, lokacin da ma’aikatan ke kokarin hana samarin kwasar man fetur daga wata tankar mai data fadi, a yankin Sabo Market, dake hanyar Ogbomosho, a jiya Laraba, don kare lafiyar su.Rahotanni sun bayyana cewa wata motar dakon man fetur din data fadi ta dauko mai lira dubu 33, wanda ta jirkice bayan tayar ta tayi bindiga tare da fara zubar da Mai, daga bisani kuma ta kama da wuta.

Daily trust, ta rawaito cewa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, sun kai dauki akan lokaci don hana samun asarar rayuka, tare da samun dauki daga masu kashe gobara na jihar Kwara.

Sai dai abin takaici shine mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya sanar da cewa jami’an su sun gamu da abin tarnaki lokacin da suke kokarin kare rayuwar al’umma a jihar ta Oyo, ta hanyar jifan su da masu diban fetur suka rika yi da duwatsu, da kuma lalata musu motar kashe gobara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here