Jami’an tsaro sun karbe iko da sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa bayan barkewar rikici

0
63

Rahotanni sun shaida cewa tuni Jami’an tsaro suka karbe ikon sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa bayan barkewar rikici a lokacin taron kwamitin amintattu na jam’iyyar daya gudana a birnin tarayya Abuja

Rikicin ya samo lokacin da aka hana Sunday Ude-Okoye, shiga wajen taron.

Jam’iyyar dai ta afka cikin rikicin shugabanci saboda kowa daga cikin Samuel Anyanwu da Ude-Okoye, na ikirarin zama halastaccen sakataren PDP, na kasa.

:::Rayuwa ta tana cikin hatsari saboda tallafin da ake cewa an bani na Miliyan 20 da Gida—Hussaina Matar Seaman Abbas

Jaridar Vanguard, ta rawairo cewa yan bangar siyasa masu goyon bayan mutane biyun ne suka tayar da hargitsi, a sakatariyar.

Shugaban kwamitin amintattu na PDP, Sanata Wabara, ya nemi daukacin yan jam’yyar su manta da banbancin dake tsakanin su don sake gina ta, don inganta Nigeria.

Shima shugaban PDP, na kasa Umar Damagum, ya zargi manyan jiga-jigan, jam’iyyar da rura wutar rikicin dake gudana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here