Rayuwa ta tana cikin hatsari saboda tallafin da ake cewa an bani na Miliyan 20 da Gida—Hussaina Matar Seaman Abbas

0
87

Hussaina matar Seaman Abbas, sojan ruwan Nigeria da aka kulle saboda karya dokar aiki ta bayyana yadda ta shiga kunci da damuwa tare da fuskantar barazana akan zargin da aka yi mata cewa ta karbi kudin tallafi Naira Miliyan 20, da Gida, da mota sakamakon yadda al’umma suka tausaya mata da mijin ta bayan abin daya faru da mai gidan nata, a hannun rundunar sojin ruwa na rufe shi tsawon shekaru.

:::Wani jirgin sama ya yi hatsari a filin jirgin saman Abuja

Daily News24, ta rawaito cewa, Hussaina, ta bayyana halin da take ciki bayan fitar da wani faifan bidiyon da tayi, tare da cewa a yanzu haka tana cikin halin rashin lafiya tsawon lokaci, inda tace tana bukatar tallafin al’umma wajen samun tallafin kudin da akeyin ikirarin an bata.

Cikin sakon data fitar Hussaina, ta godewa al’ummar da suka jajanta mata lokacin da iftila’in daya rafu da mai gidanta, tare da godewa al’ummar jihar Kano.

Bayan haka tayi rantsuwa da Allah akan cewa taimakon da ake cewa El-Rufa’i ya bata bai zo hannun ta, har ma da sauran taimakon da ake yada cewa ta samu.

Kawo wannan lokaci tace bata tare da mijin ta, da ‘ya’yanta, kuma ta bar jihar Gombe da zama.

Idan za’a iya tunawa Hussaina, itace ta shige gaba wajen samarwa da mijin ta yanci bayan ya aikata laifin da ya sanya aka kulle shi a hannun rundunar sojin ruwan Nigeria.

Bayan samun yancin mijin nata ne rundunar sojin ta sallame shi daga aiki, bisa yin duba da ka’idodjin aikin su.

Haka zalika an samun yada labaran cewa Hussaina, ta samu tallafin kudade daga al’umma har da mota da gida, da a yanzu ta tabbatar da cewa bai zo wajen ta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here