Fadar Shugaban Kasa ta caccaki tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dangane da maganganun da yayi akan jam’iyyar APC da Gwamnatin Bola Tinubu.
A ranar litinin ne El-Rufai, a yayin wani taron kasa daya gudana a Abuja kan karfafa dimokuradiyya a Najeriya, ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta gaza cika alkawuran da ta dauka ga ‘yan kasa.
Ya ce: “Ba na ganin APC a matsayin jam’iyya. Ba a yi taro na kowanne bangaren jam’iyya ba, cikin shekaru biyu —ba taron shugabanni, ba taron kwamitin koli, ba komai. Ba mu San ko mutum daya ne ya mamaye jamiyyar ba”
Tsohon gwamnan Kaduna ya bayyana cewa akwai tazara mai yawa tsakanin jam’iyyar da mutane, yana mai cewa jam’iyyar ta sauka daga tsarin da aka kafa ta akai, kuma ba za ta iya cika alkawuranta ga jama’a ba, musamman magance matsalolin Nigeria.
Ya kara da cewa matsalolin da kasar ke fuskanta sakamakon shugabanci ne na jahilai da wanda ba su da ilimi mai zurfi da ke rike da madafun iko.
A martanin Mai Baiwa Shugaba Bola Tinubu Shawara Kan Harkokin Sadarwa, Daniel Bwala, ya zargi El-Rufa’i, da shirin kifar da gwamnatin da ya taimaka wajen kafawa.
A shafinsa na X, Bwala ya tambayi ko El-Rufai zai iya fadin irin wadannan kalamai idan yana cikin majalisar ministocin wannan gwamnati.