APC ba zata iya gyara Nigeria ba—Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i

0
106

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yace gwamnatin APC, karkashin Bola Tinubu, ba zata iya gyara tabarbarewar al’amuran Nigeria ba.

El-Rufai, ya kuma nuna damuwar sa game da zargin cewa gwamnatin na yiwa jam’iyyun adawa zagon kasa da nufin guguza tasirin su.

Tsohon gwamnan yace akwai garari a tsarin ingancin mulki da shugabancin Nigeria, yana mai cewa yanayin mulkin tarayya na cikin tsaka mai wuya.

:::Matatar Dangote ta siyo danyen Fetur daga kasar Amurka

El-Rufa’i, ya kasance na gaba-gaba wajen kafa APC, tun kafin ta karbi mulkin Nigeria, wanda ya zama daya daga cikin mutanen da suka dage sai Tinubu, ya samu takarar shugabancin kasa don karbar mulki daga hannun Buhari.

Sai dai a yanzu haka yana fuskantar matsin lamba tunda daga jihar sa ta Kaduna, har matakin kasa a fannin siyasa sakamakon cewa baya samun abinda yake bukata a cikin tafiyar gwamnatin tarayya, tun bayan da majalisa taki amincewa ya zama daya daga cikin ministocin Tinubu.

Tsohon gwamnan yace a halin yanzu babu wani abun a zo a gani a tsarin siyasar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here