Sabani ya biyo bayan yunkurin kafa kwamitin sulhu na addinin muslinci a jihohin kudu maso yamma

0
62

Shugabannin al’ummar musulmai da kristocin johohin kudu maso yammacin Nigeria, sun samu wata rashin fahimta a jiya litinin dangane da batun samar kwamitin sulhu na addinin muslinci a jihohin da suka hadar da Ogun, Osun, Ondo, Ekiti, Oyo, da Legas, wanda majalisar koli ta addinin muslinci ta shirya yin hakan.

:::Hadi Sirika ya bayar da kwangilar Naira biliyan 2.8 ta gyara filin jirgin Katsina ga Kamfanin da bai Cancanta ba

Wannan abu yazo a daidai lokacin da masu rajin are addinin muslinci dake yankin suka ce babu gudu babu ja da baya akan yunkurin su na kafa kwamitin da zai rika yin sasanci da sulhu a tsakanin musulman su.

Shugaban majalisar koli ta addinin muslinci na jihar Ekiti, Dr. Hammed Bakare, ya shaidawa jaridar Punch, cewa babu abinda zai hana kafa kwamitin duk da cewa wasu da ba musulmai ba basa son hakan.

Sai dai kwamishinan shari’ah na jihar Ekiti, Dayo Apata, ya sanar da cewa dokokin jihar basu amince a kafa makamancin kwamitin sulhu na musulmai ba, ko wata kotun muslinci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here