Hadi Sirika ya bayar da kwangilar Naira biliyan 2.8 ta gyara filin jirgin Katsina ga Kamfanin da bai Cancanta ba

0
69

Babbar kotun tarayya dake Abuja, ta cigaba da zama kan shari’ar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, ta shigar da tsohon ministan sifurin jiragen sama, Hadi Sirika, kan zargin sa da almundahanar naira biliyan 19.4, a zamanin tsohuwar gwamnatin Buhari.

:::Kotu ta hana yan sanda kama shugaban hukumar yaki da cin hanci ta Kano Muhyi Magaji

Yayin zaman kotun daya daga cikin shaidun hukumar EFCC, a shari’ar ya bayyanawa kotu cewa Sirika, ya bayar da kwangilar gyara filin tashi da saukar jiragen sama na jihar Katsina ga wani kamfanin da bai cancanta ba akan kudi naira biliyan 2.8.

Mai bayar da shaidar ya kasance tsohon shugaban sashin siyayyar kayayyaki na ma’aikatar sifurin jiragen sama, mai suna Musa Obinyan, wanda ya sanar da kotu cewa kamfanin Al Buraq, shine wanda aka bawa kwangilar kuma bai cancanta ba.

Musa, ya kara da cewa an yi abubuwan da basu dace ba yayin bayar da kwangilar wadda yace an nemo kudin aikin daga wani waje sannan aka bawa kamfanin.

Tun da farko EFCC, tana zargin Sirika, da aikata laifuka 10, da suka danganci bayar da kwangiloli ga kamfanoni 2, da basu dace ba, cikin su har da kamfanin kanin sa mai suna Enginos, haka ne yasa aka gurfanar da Sirika, tare da ‘yar sa mai suna Fatima.

Zuwa yanzu Kotu ta jingine sauraron shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Maris, 2025

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here