Gwamnatin Nigeria ta kashe Naira biliyan 9 wajen gyaran layin lantarkin arewa daya lalace

0
44

Gwamnatin tarayya ta ce sai da ta kashe naira biliyan 9, sannan aka samu nasarar gyara turken lantarki na Shiroro, Mando da Kaduna.

Ministan Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan.

:::Jam’iyyar NNPP ta kori tsohon kakakin ta na jihar Kano

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da ma’aikatar lantarkin ta fitar mai dauke da sanya hannun kakakin ta, Bolaji Tunji.

Turken lantarkin shine wanda ya durƙushe a watan Nuwamba a shekarar data gabata, da hakan ya kawo daukewar lantarki ta tsawon lokaci a jihohin Arewa 17.

Sanarwar ta kara da cewa har kawo wannan lokaci ba’a kai ga kammala aikin gyaran layin lantarkin daya lalace ba.

Idan za’a iya tunawa ministan lantarki Adelabu, yace za’a cigaba da fuskantar durÆ™ushewar babban layin lantarkin kasar nan, saboda har yanzu gwamnati bata kammala gyaran sa ba, bayan lalacewar da yayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here