Jam’iyyar NNPP ta kori tsohon kakakin ta na jihar Kano

0
60

Jam’iyyar NNPP ta kori tsohon kakakin ta na jihar Kano, Musa Nuhu’Yankaba.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da shugabannin jam’iyyar na mazabar Kawaji dake karamar hukumar Nassarawa.

 Sanarwar ta ce, an kori Musa Nuhu ‘Yankaba daga NNPP saboda cin amanar jam’iyyar da ake zargin ya aikata.

Korar tasa tazo bayan da aka zabi Musa Nuhu ‘Yankaba a matsayin Sakataren jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari, ba mai littafi ba, a jihar Kano.

Sanarwar ta kara da cewa an nemi ya zo ya kare kansa akan zargin cin amanar amma yaki amsa gayyatar da akayi masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here