Tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu, yace babu jiha guda daya a arewa da take da kaso 50, na malaman da suka cancanci koyarwa a makarantu.
:::Hatsarin mota ya kashe mutane 15 a jihar Kwara
Babangida Aliyu, ya bayyana hakan ne a yau Alhamis lokacin da yake yin jawabi a wajen wani taron tattaunawa da jaridar Daily Trust, ta shirya wanda aka yiwa take da ‘samar da isasshshen abincin da kasa ke bukata’ A farashi mai sauki kuma wadatacce” wanda aka gudanar a cibiyar gudanar da taro dake shalkwatar rundunar sojin sama a Abuja.
Tsohon gwamnan ya kuma nuna shakku kan hikimar da ke tattare da rufe kan iyakokin kasar nan.
Aliyu, ya roki ma’aikatar kiwon dabbobi ta tarayya da ta hada hannu da jami’o’in ilimi dana aikin gona, don ilimantar da manoma dabarun aikin noma a zamanance.
Ya ce, “Mene ne muhimmancin rufe iyakokin? Menene mahimmancin hakan alhalin yawan al’ummar Najeriya kusan adadin sauran mambobin ECOWAS ne? Kuma duk kasuwar da ka je a kasashen ECOWAS za ka gano cewa fiye da rabin abubuwan da ke wannan kasuwa daga Najeriya suke.
Ya jaddada cewa babu malaman da suka cancanci koyarwa a arewa, da kaso 50, inda yace tabbas arewa na bukatar ilimi domin samarwa kanta rayuwa mai cike da sha’awa.