Wani hatsarin daya afku tsakanin wata babbar mota (Trailer), da wata motar yayi sanadiyyar mutuwar mutane 15, a yankin Olowo a babbar hanyar Ilorin zuwa Jebba, a jihar Kwara.
Daily News24, ta rawaito cewa bayan wadanda suka rasu an samu mutane da dama wanda suka ji manyan raunika a hatsarin.
:::Sabuwar Gobara ta tashi a birnin Los Angels na Amurka
Wani mutum da lamarin ya afku a gaban idon sa ya shaidawa manema labarai cewa motocin da suka yi hatsarin sun hadar da babbar motar dauko kaya da kuma motar fasinjoji ta yan kasuwa.
Majiyar tace motocin suna tafiya a hannun titi biyu, amma duk da haka sai da suka yi taho mu gama da misalin karfe 6, na yammacin jiya Laraba.
Daya daga cikin motocin ta dauko shanu da mutane da za’a kai su Ogbomoso dake jihar Oyo, sai kuma motar trailar da take hanyar Lagos zuwa Kano.
Jami’an yan sandan da suka yi gaggawar zuwa wajen da lamarin ya faru sun kai mutanen da suka jikkata zuwa asibiti.
Mai magana da yawun hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa reshen jihar Kwara, Muftahu Irekeola, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai yi karin bayani akan yadda hatsarin ya faru ba.