An gurfanar da wani mutum mai shekaru 43, bisa zargin sa da yin kutse a na’urar hada-hadar kudi ta Moniepoint, tare da sace naira biliyan 1, da miliyan 190,728,076.
:::Gwamnatin Thailand ta amincewa Daruruwan mutane sun yi auren jinsi
An gurfanar da mutumin mai suna Sunday Ozimede, a babbar kotun jihar Lagos.
Rundunar yan sandan jihar Lagos, sashin binciken almundahanar kudade ne suka gurfanar da shi akan zargin yin kutse, da samun kudi ta hanyar da bata halasta ba.
Lauyan dake kare hukumar yan sanda a shari’ar, Justine Enang, yace wanda ake zargi yayi kutse a manhajar adana bayanai ta bankin Moniepoint, a watan mayun shekarar 2024, har ya samu damar sace kudaden, ta hanyar nadar bayanan manhajar.
Enang, yace wanda ake zargi tare da abokan aikin sa sun sace naira 945,728,076, sannan hakan yasa an kara sace wata naira 145, sakamakon kutsen nasu.
An bayyanawa kotun cewa anyi amfanin da manyan na’urorin kutse, da hakan ya sanya ake fargabar yiwuwar cigaba da yin kutse a asusun ajiyar kudin mutane a Nigeria.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumar sa da aikatawa. Yayin da lauyoyin dake kare shi suka nemi beli, a daidai lokacin da masu shigar da kara suka kalubalanci bayar da belin bisa hujjar cewa Ozimede, zai iya gujewa shari’ah
Kawo yanzu alkalin dake sauraron shari’ar Adetokunbo Banjo, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Maris na wannan shekara, don sauraron bukatar bayar da belin tare da bayar da umarnin tsare wanda ake zargi da satar a gidan yari.
Kamfanin Moniepoint, ya tabbatarwa da masu hulda dashi cewa hakan ba zai sanya dukiyar su a cikin hatsari.