Jirgin saman kasar Sierra Leone ya dawo zuwa Nigeria bayan shekaru 15

0
44

Kamfanin jirgin saman Air Sierra Leone, ya dawo yin jigilar al’umma a tsakanin jihar Lagos ta Nigeria da birnin Freetown, bayan kwashe shekaru 15, da dakatar da zirga-zirgar sa daga Freetown zuwa Lagos, kai tsaye.

:::Likitoci sun bukaci jami’an gwamnati su rika zuwa ana duba su a asibitin Abuja

Air Sierra Leone, ya dawo Nigeria ne ta hanyar hada kai da wani kamfanin jirgi dake aiki a Nigeria mai suna XEJet.

XEJet, ya kasance mai kula da lafiyar jiragen Saliyo, sannan ya bayar da jirage 3, da za’a cigaba da hada-hada tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin jirgin Air Sierra Leone, ya bayyana farin cikin sa akan yadda aka cigaba da hada-hadar kasuwanci tsakanin kasar su da Nigeria, kamar yadda shugaban kamfanin Edward Lacle, ya sanar a jihar Lagos, ranar Laraba, lokacin da aka kaddamar da cigaban huldar.

Ya sanar da yan Jarida cewa kamfanin Air Sierra Leone, ya samu damar yin jigilar kwanaki uku a Nigeria tsakanin Litinin, Laraba, da Juma’a, inda yace za’a kara yawan jigilar nan da wani lokaci kankani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here