Likitoci sun bukaci jami’an gwamnati su rika zuwa ana duba su a asibitin Abuja

0
44

Likitocin birnin tarayya Abuja dake cigaba da yajin aiki a yanzu haka sun nemi manyan jami’an gwamnatin tarayya su rika zuwa asibitocin gwamnati ana duba lafiyar su, don su san irin halin da asibitocin ke ciki na rashin samun kulawar data dace.

Likitocin sun ce marasa lafiya na dandana kudar su saboda gazawar gwamnati wajen kulawa da asibitocin.

:::Shugaban Amurka ya nemi Rasha ta kawo karshen yakin ta da Ukraine

Daga cikin wadanda likitocin suka nemi su rika zuwa asibitocin akwai ministan Abuja, Wike, da shugaban majalisar dattawa Akpabio.

Shugaban kungiyar likitocin Abuja, George Ebong, yace in har da gaske ana son gyara bangaren lafiya, to ya zama wajibi jami’an gwamnati su rika zuwa asibitocin gwamnati ana kula da lafiyar su, kamar yadda ya sanar lokacin da yake zantawa da tashar talbijin ta Channels.

Shugaban kungiyar yace ba za’a taba gyara asibitocin Abuja ba, in har shugabannin majalisar dokokin kasa da ministan Abuja, basa zuwa asibitocin gwamanti ana duba su.

Yajin aikin da likitocin Abuja suka fara ya biyo bayan karewar wa’adin mako uku da suka bawa gwamnatin tarayya ta biya musu wasu hakkokin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here