CBN zai kawo karshen cinkin takardar kudi ta Naira

0
91

Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN, Dr. Olayemi Cardoso, ya kudiri aniyar dakile cinikin takardar kudi ta Naira da hakan ya zama ruwan dare a fadin Nigeria.

Gwamnan ya sanar da hakan ne lokacin da yake jawabi a wani taron shugabannin bankunan kasuwanci da masu ruwa da tsaki, wanda ya gudana a jihar Lagos, inda aka yiwa taron lakabi da “Cinikin takardar kudi ta Naira.”

:::Kungiyar kwadago ta nemi ministan lantarki yayi murabus

Gwamnan ya bayyana daukar matakin ta bakin babban mataimakin sa Fatai Kareem, inda yace siyar da takardar kudi ta naira da wasu keyi musamman jami’an bankuna yana da tasiri mummuna ba ga bankuna kadai ba har da rayuwar yan Nigeria ta yau da kullum wadanda suka dogara da yin al’amuran su da tsabar takardun kudi.

A nasa jawabin shugaban taron Abraham Aziegbe, yace tabbas cinikayyar naira da akeyi ya haddasa karancin takardun kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here