NDLEA ta kama matasa masu safarar miyagun kwayoyi a Jihar Kano

0
22

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta kama wasu matasa Musa Usman, dan shekara 25, da Bashir Ya’u Bashir, mai shekaru 24, bisa zargin su da mallakar kayayyakin maye da miyagun kwayoyi, a shatale-talen Rahama, dake karamar hukumar Bebeji, a ranar 20, ga watan Junairu 2025.

:::Kamfanin NNPCL ya kara farashin litar fetur

Cikin kayan laifin da aka samu a wajen su akwai tabar wiwi mai nauyin kilogram 1.1, sai kwayar Diazepam, kwanso 38, mai nauyin gram 8, da kwayar Exol, kwanso 165, mai nauyin gram 59.

A yayin da jami’an NDLEA, ke kokarin kama wadanda ake zargin daya daga cikin su mai suna Musa Usman, ya farmaki daya daga cikin ma’aikatan wanda ya ji masa rauni da Danbuda.

Kwamandan hukumar na Kano, Abubakar Idris Ahmad CN, ya yi ala wadai da abin da masu laifin suka aikata tare shan alwashin tabbatar da doka da kuma kiyaye lafiyar jami’an su, inda ya kara da cewa farmakar jami’an su a bakin aiki ba zai karya gwuiwar su ba, a kokarin kakkabe bata gari, da kuma tsaftace al’umma daga ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Kwamandan ya kara da cewa baki dayan matasan suna hannun NDLEA, kuma zasu gurfana a gaban shari’a, akan tuhuma biyu ta kayan maye da raunata jami’in hukumar, kamar yadda wata sanarwa mai dauke sanya hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Sadiq Muhammad Maigatari, ta bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here