Kamfanin man fetur na Nigeria NNPCL, ya sanar da karin farashin litar man Fetur a jihar Legas da birnin tarayya Abuja.
Yanzu haka an koma siyar da kowacce lita daya akan farashin naira 965, a Legas sai Abuja, da farashin ya koma naira 990, wanda wannan ne yake nuna cewa an samu karin naira 25, a Abuja, sai naira 35, a Legas, wanda kamfanin ya dora alhakin karin akan tsadar da danyen man yayi a kasuwannin duniya.
:::An kama ma’aikacin KEDCO ya sace mitar wutar lantarki
Kafin karin ana siyar da lita daya akan farashin naira 965, a Abuja, Legas kuma naira 925, kan kowacce lita.
Kawo wannan lokaci kowacce gangar danyen fetur daya ta kai dala 80, sabanin dala 73, da ake siya a baya.
Idan za’a iya tunawa a kwanan nan ne NNPCL, ya sanar da rage farashin litar man a gidajen man sa na Abuja, da jihar Legas.