Tankar mai ta kuma faduwa a jihar Niger, mutane sunje ɗiban ganima

0
39

Tankar mai ta kuma faduwa jihar Niger, inda mutane suka je ɗiban ganima, kwanaki biyu bayan irin wannan abu ya afku da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 96.

Motar man fetur din ta fadi a yau litinin a birnin Bida.Wani faifan bidiyon da yake yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda matasa ke kokarin kwasar man dake kwarara daga motar dakon man.

Sai dai wasu mutanen sun gudu daga wajen da motar ta fadi don gujewa faruwar makamancin iftila’in da ya afku ranar asabar a yankin Dikko Junction.

Wani mai suna Yunusa, da jaridar Premium Times, ta zanta dashi ya bayyana mamakin sa akan yadda mutane basa jin tsoron motar ta kama da wuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here