Cutar Anthrax ta shigo Nigeria

0
75

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa an samu bayyanar cutar Anthrax, mai kama dabbobi da mutane a jihar Zamfara.

Haka ne yasa ma’aikatar kula da harkokin daddobi ta kasa ke jan hankalin al’umma da su zamo masu lura da kiyayewa akan duk wani abun da ka’iya sanyawa a kamuwa da cutar, wadda tuni an tabbatar da samun ta a Zamfara.

:::Masu hulda da kamfanonin sadarwa zasu kai karar NCC saboda karin kudin kira da Data

Shugaban sashin yada labarai na ma’aikatar Ben Goong, ya fitar da wata sanarwa da yake cewa akwai bukatar rage hatsarin kamuwa da Anthrax, da kuma yaduwar ta.

  1. Cutar anthrax, cuta ce wadda ƙwayar cutar bacterium Bacillus anthracis ke kama dabbobi irin su shanu da awakai da ma mutane, inda take saka musu cutukan da wani lokacin ke hallaka wanda ta kama.
  2. Wasu daga cikin alamomin cutar sun hadar da zazzaɓi, tari, amai da gudawa, bushewar maƙogwaro, ciwon kai da ƙaiƙayi.

Sanarwar da ma’aikatar kula da dabbobin ta fitar tace za’a iya dakile yaduwar cutar ta hanyar yiwa dabbobin dake cikin hatsarin kamuwa da ita rigakafi, ko kuma yiwa wadanda suka kamu magani cikin gaggawa, tare da cewa wannan ce kadai hanyar dakile yaduwar ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here