Gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar gina titin Abuja zuwa Kaduna ga Kamfanin da ya dena aiki

0
86

Wani binciken da jaridar Daily Trust, ta gudanar ya bankado cewa Gwamnatin tarayya ta sake bayar da kwangilar gina sashin da ba’a kammala ba, a aikin titin Abuja zuwa Kaduna ga wani kamfani daya daina aiki tun lokaci mai tsawo.

:::Donald Trump ya haramta bawa wadanda aka haifa a Amurka shaidar zama ɗan ƙasa

An dai bayar da kwangilar akan kudi naira biliyan 252.89.

Idan za’a iya tunawa a kwanakin da suka gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da kwace aikin gina titin daga hannun kamfanin Julius Barger, saboda samun sabani akan farashin da za’a kammala aikin sakamakon tashin farashin kayayyakin sarrafawa, sannan aka sanar da mayar da kwangilar titin zuwa kamfanin Infoquest Nigeria Limited.

Tuni dai bincike ya bankado cewa kamfanin Infoquest Nigeria Limited, ya kai matakin da hukumar CAC, mai yiwa kamfanoni rijista ka’iya soke lasisin sa, saboda jarin da yake amfani dashi bai wuce naira dubu 100, ba.

Ministan Ayyuka, David Umahi, ya sanar cewa Infoquest ne kamfanin da ya yi nasarar samun aikin daga cikin kamfanonin da suka nemi karbar ragamar karasa titin bayan samun tangarda tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanin Berger.

Tsohuwar gwamnatin shugaban Nigeria, Buhari ce ta bayar da aikin gina titin daya taso daga Abuja zuwa jihar Kano, wanda karyewar darajar naira tasa kamfanin Berger gaza kammalawa.

A yanzu dai gwamnatin tarayya ta hannun ministan ayyuka Dave Umahi, tace kamfanin Infoquest Nigeria Limited, ya karbi ragamar karasa aikin akan kudi naira biliyan 252.89.

A makon jiya ne Ministan Ayyuka David Umahi ya bayyana cewa Kamfanin Infoquest Nigeria Limited ya yi nasarar samun aikin a kan Naira biliyan 252.89, bayan an ƙwace daga hannun Julius Berger.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here