Gwamnatin Kano tayi alkawarin zamanantar da tashar talbijin ta ARTV

0
50

Kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada aniyar sa ta ganin an daga likkafar tashar talbijin ta ARTV, don zama daidai da tashoshin talbijin da ake alfahari dasu a Nigeria.

Waiya, ya bayyana hakan ne lokacin ziyarar ma’aikatan tashar talbijin ta ARTV, inda ya sanar da cewa akwai bukatar a samar da kayan aiki na zamani ga tashar wanda haka ne zai bawa ma’aikatan ta damar yin aikin da zai kara fito da darajar tashar.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan sashin ayyuka na musamman na ma’aikatar, Sani Abba Yola, ya sakawa hannu.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa za’a bayar da fifiko wajen samar da walwalar ma’aikatan tashar, inda ya nemi a samar da wata Kungiyar taimakawa juna tsakanin ma’aikatan ARTV, yana mai cewa zai goyi bayan hakan sosai da kuma bayar da gudunmuwar sa ga tsarin.

Da yake nasa jawabin mataimakin shugaban tashar talbijin ta ARTV, Alhaji Idris Abba, ya taya Waiya, murnar samun mukamin kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano, tare da bayyana masa irin kalubalen da tashar ke fuskanta, musamman rashin tsayayyiyar wutar lantarki, da Kuma motocin da suka lalace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here