Matashi ya kashe mahaifiyar sa saboda tsafin yin arziƙi

0
110

Wani matashi mai suna Samuel Akpobome, ya kashe mahaifiyar sa tare da yin lalata da gawar ta, saboda cewar zai yi arziki in har ya aikata wannan mummunan danyen aiki.

Matashi dan shekara 18 ya kasance dan asalin jihar Edo, dake kudancin Nigeria.

Tuni dai matashin ya shiga hannun jami’an tsaro, inda ya shaidawa ‘yan sandan jihar Edo cewa, ya kashe mahaifinyar tasa mai suna Christiana domin ya yi tsafin samun kudi da ita.

Samuel, ya bayyanawa yan sanda cewa da asubahi ya shiga dakin babar tasa ya shake mata wuya har sai da ta daina numfashi, bayan haka kuma ya cire kayan jikin ta yayi lalata da gawar ta.

Matashin ya bayyana cewa, wani boka mazaunin garin Oghara, ne ya umarce shi da cewa matukar zai iya kashe mahaifiyarsa sannan ya yi lalata da gawarta, Kuma ya killace gawarta har tsawon kwana biyu, zai zama babban mai arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here