Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa akan sauya fasalin dokar harajin Nigeria, Taiwo Oyedele, ya sanar da cewa za’a fara amfani da sabon tsarin karÉ“ar haraji a watan Yulin shekarar da muke ciki.
Taiwo Oyedele, yace majalisun dokokin kasa zasu amince da kudirin dokar harajin kafin watan Maris na wannan shekara ta 2025.
Yace za’a bawa masu biyan haraji lokaci mai tsaho don suyi shirin fara biyan harajin kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, bayan majalisa ta sahale yin amfani da dokar.
Kalaman Oyedele, sun zo kwanaki kadan bayan da Kungiyar gwamnonin Nigeria NGF, ta amince da kudirin dokar harajin, duk da cewa ta nemi a yi gyara a bangaren karbar harajin VAT.
Kafin amincewar kungiyar NGF, wasu daga cikin gwamnonin Arewa sun nuna damuwa akan dokar tare da shan alwashin kin amincewa da ita, musamman gwamnonin Kano, Bauchi da Borno.
Haka zalika wasu daga cikin yan majalisar arewa sun bayyana kin amincewa da kudirin dokar harajin, tare da cewa dokar zata jefa arewa a bakin talauci da kuma azurta jihar Lagos, wato mahaifar shugaban Nigeria Tinubu.