Tinubu zai rabawa mutane miliyan 70 Naira dubu 75, kowannen su

0
83
Tinubu
Tinubu

Gwamnatin tarayya ta sanar da kammala shirin rabawa yan Nigeria miliyan 70, Naira dubu 75 kowannen su, da manufar rage tasirin tsadar rayuwa da ake ciki.

Mai taimakawa shugaban kasar a fannin hulda da jama’a, Hon. Aliyu Audu, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar a jiya lahadi, yana mai cewa hakan na daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu, na kokarin rage talaucin da yan Nigeria ke fama da shi.

Audu, ya kuma ce shugaban kasar, ya aiwatar da wasu abubuwan da zasu nunawa al’umma cewa yayi kokari a shugabancin Nigeria a tsawon watanni 19, da suka gabata.

Mai taimakawa shugaban kasar, yace manufofin gwamnatin Tinubu, sun haifarwa da Nigeria Sakamako mai kyau a cikin gida da ketare, wanda a cewar sa hakan ya kawo sanadiyyar samun masu zuba hannun jari a kasar nan daga kasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here