Fadar shugaban Nigeria tace ko kadan babu gaskiya a zargin da wasu keyi na cewa gwamnatin Tinubu, ta tilastawa tsohon shugaban Nigeria Buhari, gurfana a gaban kotun Faransa, don bayar da sheda akan kwangilar aikin wutar lantarkin Mambila, akan kudi dala biliyan 6.
Mai bawa Shugaban kasa shawara a fannin yada Labarai da Tsare tsare, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya sabar, mai lakabin (Tinubu bai ce dole tsohon Shugaban Nigeria Buhari sai ya gurfana a gaban kotun Paris ba).
Amman fah sanarwar bata musanta labarin zuwan Buhari gaban kotu ba, inda take cewa duk mutanen da suka amince su bayar da sheda akan shari’ar suna yi ne saboda son ransu.
A jiya asabar ne, wata kafar labarai ta yanar Internet, ta wallafa rahoton cewa tsohon shugaban Nigeria, Buhari ya samu gayyata a gaban wata kotun Paris domin bayar da sheda akan wata shari’a da ta shafi kwangilar wutar lantarki ta Mambilla ta tsabar Kudi har dala biliyan 6.
Labarin farko da aka fitar ya nuna cewa tilastawa tsohon shugaban kasa Buhari, akayi akan zuwa Paris domin bayar da sheda akan kwangilar samar da wutar lantarki da aka bawa kamfanin Sunrise Power da Kuma kamfanin TCN, na kasar nan, a lokacin mulkin tsohon shugaban hugaban kasa Olusegun Obasanjo a shekarar 2003.
Har ila yau, rahoton ya yi ikirarin cewa Buhari ya fuskanci tambayoyin tsawon lokaci a gaban kotun a ranar asabar, tare da cewa za:a ci gaba da sauraron jawabin sa a yau lahadi, a gaban kotun sasanta harkokin kasuwanci ta Faransa.
Rahoton ya zargi cewa shugaba Bola Tinubu ne ya bada umarnin cewa a tilastawa Buhari bayyana a gaban kotun don bayar da sheda.
Amman fadar shugaba Tinubu, tace wannan zargi bashi da tushe ballantana makama.