An samu hatsarin wata tankar mai wadda ta faɗi tare da kamawa da wuta nan take a daidai gidan man Badeggi da ke Dikko Junction a ƙaramar Hukumar Gurara ta jihar Neja, dake kusa da kan titin Kaduna zuwa birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun ce mutane da dama sun rasa rayukansu, sai dai har izuwa wannan lokaci babu haƙiƙanin adadin mutanen da hatsarin ya shafa daga hukumomin yan sanda ko masu kashe gobara.
Fashewar tankar mai dai ta zama wata hanyar mutuwar mutane a Nigeria, daga kudu har arewacin kasar saboda babu wata hanyar jigilar man fetur dole sai ta hanyar manyan motoci.
Rashin kyawun tituna da tukin ganganci na daga cikin dalilin samun hatsarin tankar man.
Idan za’a iya tunawa ko a watannin baya sai da fashewar tankar mai tayi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 200, a majiya dake jihar Jigawa.