Manoman hatsi a jihar Niger, sun bayyana damuwar su akan yadda farashin kayan da suka noma yayi mummunar faduwa a kasuwanni sabanin yanda suka yi zaton samun riba.
Rahotanni sun bayyana cewa a yanzu haka farashin kayan abinci a jihar ta Niger, na cigaba da faduwa fiye da tunani.
Manoman sun ce hakan baya rasa nasaba da yadda kamfanoni suka koma shigo da abubuwan da suke sarrafawa daga ketare wanda a baya suke siya a hannun manoman cikin gida.
Jaridar Aminiya, ta rawaito cewa shugaban kungiyar manoma ta Amana, reshen Shiroro, Hassan Ango Abdullahi, yace tabbas kayan abinci sun yi sauki a kasuwannin jihar Niger.
Ya bayyana cewa kamfanoni yanzu sun fi son sayen kaya daga ƙasashen Chadi da Ghana da wasu ƙasashe saboda farashin su yafi na Nigeria sauki.
Abdullahi, yace buhun wake da a baya ake siyar da shi akan naira dubu 105, yanzu ya koma naira dubu 80.
Kawo wannan lokaci dai manoma da yan kasuwa sun nuna damuwa akan faduwar farashin, yayin da sauran al’umma ke bayyana farin cikin su da saukin rayuwa da aka fara samu.