Nigeria ta shiga kungiyar BRICS

0
58

Kasar Brazil mai shugabantar kungiyar BRICS, a wannan shekara, ta sanar da cewa Nigeria shiga kungiyar, wadda ta fara daukar hankali a duniya baki daya.

Gwamnatin kasar Brazil, ta kasance mai rike da tafiyar da al’amuran shugabancin kungiyar BRICS, a wannan shekara ta 2025, tace a yanzu Nigeria tana bayar da muhimmanci a fannin karfafa hulda da kasashen kudancin duniya, wanda ita Brazil, ke mutunta hakan.

Sanarwar da Brazil, ta fitar tace kasancewar Nigeria, mai karfin tattalin arziki a Afrika, da kuma yawan al’umma, wanda hakan zai yi tasiri ga kawancen BRICS.

Kasashen da suke cikin BRICS, sun hadar da Brazil, Rasha, Indiya, China, Afirka ta kudu, Egypt, Ethiopia, Indonesia, Iran da HaÉ—aÉ—É—iyar Daular Larabawa.

Manufofin kungiyar suna nuna adawa da wasu manufofin tattalin arzikin kasashen yammacin duniya, da kuma Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here