Yanayin tattalin arzikin Nigeria, na cigaba da samun tagomashi kamar yadda shugaban kasar Bola Tinubu, ke bayyanawa inda yace sauye sauyen tattalin arziki da yake dauka ne suka kawo haka, a daidai lokacin da yan kasar ke cewa tattalin arzikin su ya lalace saboda manufofin gwamnatiin.
Ana tsaka da haka ne Bankin Duniya, sanar da cewa akwai yiwuwar Nigeria ta samun karuwar tattalin arzikin ta da kaso 3.6 a shekarar 2025 zuwa 2026.
Bankin Duniya ya sanar da wannan cigaba da Nigeria ka’iya samu a bangaren tattalin arziki, cikin wani rahoton da ya saba fitarwa wanda ya shafi tattalin arzikin kasashen duniya.
An fitar da rahoton ne a jiya alhamis, wanda ya mayar da hankali wajen bayyana yanda tattalin arzikin duniya zai kasance a shekarar 2025.
Rahoton yace yankin Afrika mai hamada zai samu tagomashin tattalin arziki da kaso 4.1 a 2025, sai kaso 4.3, a shekara mai kamawa.
Rahoton, ya kara da cewa ana hasashen samun saukin hauhawar farashin kayyaki a Nigeria, wanda tun kafin yanzu shugaban kasar Bola Tinubu, shima ya ce zai yi kokarin rage farashin kayayyaki.