Tinubu ya saka harajin naira 10 akan kowacce litar man fetur

0
26
man fetur
man fetur

Kungiyar Dillalan man fetur masu zaman kansu ta kasa IPMAN, ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ta kakabawa yan Nigeria harajin naira 10 akan kowacce litar man fetur.

Shugaban IPMAN, reshen Arewacin Najeriya, Alhaji Salisu Ten Ten ne, ya bayyana hakan.

Yace matukar hukumar kayyade farashin man fetur ta Najeriya bata janye shirin ta ba na kara naira 10 a duk lita daya a matsayin haraji, to masu gidajen mai basu da wani zabi daya wuce suma su kara farashin man fetur.

IPMAN tace litar man fetur ka’iya iya kaiwa naira 1,040 ko 1,050.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here