Jami’an DSS sun sake kama Madadi Shehu

0
70

Wasu jami’an tsaron da ake kyautata zaton DSS, ne sun sake kama dan Gwagwarmaya, Mahadi Shehu, a unguwar Dosa, dake Kaduna, da misalin karfe 11:00, na safe.

Sai dai babu wata sanarwa da aka samu daga hukumomin tsaro dangane da kamen nasa, kamar yadda jaridar Daily Trust, ta rawaito.

Mahadi Shehu, ya kasance mai sharhi akan al’amuran siyasa da gwagwarmaya, wanda aka kama shi kwanaki saboda fitar da wani faifan bidiyon dake nuna cewa akwai sojojin Faransa a Nigeria.

Daya daga cikin ‘ya’yan Mahadi mai suna Buhari Mahadi, yace sun kasa samun damar zantawa da mahaifin nasu, kuma yace basu sani ba kama shi akayi ko kuma gayyatar sa aka yi zuwa wajen jami’an tsaron.

A baya dai kotun jihar Kaduna, ce ta bayar da belin sa akan naira miliyan 3, da kuma mutane 2, da suka tsaya masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here