Bafarawa ya fice daga jam’iyyar PDP

0
55

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya fice daga Jam’iyyar PDP.

Bafarawa ya sanar da ficewar tasa a yau Talata, cikin wata wasikar da ya aikewa Shugaban Jam’iyyar PDP na Ć™asa.


Bafarawa, yace zai mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’umma, musamman a yanzu da arewa ke bukatar jajirtattun mutane don magance kalubalen da yanke ke ciki.


Zuwa yanzu dai tsohon gwamnan na Sokoto, bai sanar da komawa wata jam’iyyar siyasa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here