Cutar murar tsuntsaye ta shiga jihar Kano

0
48

Gwamnatin tarayya tace cutar murar tsintsaye ta shiga jihar Kano, wanda aka tabbatar da samun ta a karamar hukumar Gwale, a birnin Kano.

::::Gwamnatin tarayya tace ba za’a dena fuskantar lalacewar babban turken lantarki ba

Gwamnatin tarayyar ta sanar da hakan cikin wata sanarwar data samu sanya hannun Dr. Taiwo Olasoju, a madadin babban mai kula da lafiyar dabbobi na kasa, inda tace akwai fargabar fantsamar cutar daga Kano, zuwa wasu jihohin Nigeria.

Murar tsuntsaye dai ta kasance cuta mai saurin yaduwa a tsakanin kaji, agwagi, zabi da talotalo, kuma tana saurin yaduwa a tsakanin dabbobin tare da kashe su ta hanyar sarke musu numfashi.

Don haka ya bukaci gwamnatocin jihohi da ofishin kula lafiyar dabbobin  jihohin su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace da kuma daƙile yaɗuwar cutar.

Sanarwar ta nemi a wayar da kan masu kiwo da kasuwancin tsuntsaye dangane da hatsarin dake tattare da cutar da matakan kariya, sannan hukumomi su riƙa sanya idanu tare da kai rahoto idan aka ga wata alama.

Shugaban Ƙungiyar Masu Kiwon Kaji ta Jihar Kano, Dr. Usman Gwarzo ya tabbatar da ɓullar cutar a karamar hukumar Gwale.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here