Gwamnatin tarayya tace ba za’a dena fuskantar lalacewar babban turken lantarki ba

0
57
wutar lantarki

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta sanar da cewa ba’a dauko hanyar magance matsalar durkushewar babban turken wutar lantarkin kasar ba, wanda ya lalace fiye da sau 10, a cikin shekarar data wuce ta 2024.

Mininstan lantarki, Adebayo Adelabu, ya sanar da hakan ranar litinin yayin da yake kare kasafin kudin ma’aikatar sa na shekarar 2025, a zauren majalisar dattawa.

Yace dole ne a rika samun daukewar babban turken lantarkin saboda har yanzu gwamnatin bata kai ga kammala gyara layukan rarraba lantarkin arewa ba, saboda ayyukan yan ta’adda.

Adelabu, yace tabbas wutar zata cigaba da lalacewa, amma zasu rage hawaitar samun hakan, inda ya kara da cewa masu lalata kayan samar da wutar ne babbar barazanar fannin lantarki.

Ministan, ya kuma sanar da shirin su na zuba naira biliyan 36, a injinan samar da lantarki a unguwannin dake fadin Nigeria, saboda a inganta rarraba wutar ga al’umma, da magance matsalolin da ake samu daga injinan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here