An gudanar da zanga-zanga a shalkwatar jam’iyyar PDP

0
60

Wasu masu zanga-zanga sun taru a shelkwatar jam’iyyar PDP ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, domin nuna rashin amincewa da kama aikin sabon sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sunday Ude-Okoye wanda kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana a matsayin halastaccen sakataren jam’iyyar.

Rahotanni sun ce a yau litinin ne sakataren jam’yyar ya fara aiki, bayan hutun da aka dawo na shekara, da yasa ayyukan ofishin jam’yyar ya tsaya zuwa yau da aka cigaba da gudanar da hada-hadar ofishin.

To sai dai masu zanga-zanga da ke goyon bayan senator Sam Anyanwu wanda ake taƙaddama a kansa sun mamaye ƙofar ofishin inda suke cewa Anyanwu ne sakataren PDP.

A baya-bayan nan ne dai kotun ɗaukaka dake Enugu ta ayyana cewa Sunday Ude-Okoye ne halastacce sakataren jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here