Eric Chelle ya zama cikakken mai horas da Super Eagles

0
68

Hukumar Kwallon kafa ta Nigeria, ta bayyana Eric Chelle, a matsayin cikakken mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Nigeria Super Eagles, a hukumance.

An gudanar da bikin bayyana mai horaswar a yau litinin, wanda aka gabatar a dakin taro na filin wasa na Moshood Abiola, dake birnin tarayya Abuja.

:::Yan majalisa sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar Lagos

A ranar talatar data gabata ne hukumar NFF, ta sanar da nada Eric, a matsayin kocin tawagar Nigeria, wanda ya zama mutum na 42, da zai jagoranci Super Eagles.

Kocin dan asalin kasar Mali, an bashi damar rike Super Eagles, don tawagar ta samun gurbin buga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here